Connect with us

News

Gwamnoni uku sun kai ƙarar Emefiele da Malami kan raina kotu

Published

on

 

Gwamnoni Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai ƙarar ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, da gwamnan Babban Bankin ƙasar Godwin Emefiele, saboda zargin ƙin bin umarnin kotun ƙolin ƙasar kan wa’adin amfanin tsofaffin takardun kuɗi.

Advertisement

 

A wata sabuwar ƙara da suka shigar gaban kotun, jihohin uku sun gargaɗi ministan shari’a na ƙasar ga gwamnan CBN ɗin kan ƙin bin umarnin hukuncin da kotun ta yanke ranar 3 ga watan Fabrairu.

Advertisement

Sarkin musulmi ya sanar da Laraba a matsayin 1 ga watan Sha’aban

Jihohin sun ce aiwatar da tsarin ya jefa al’umomin jihohinsu cikin mawuyacin hali.

 

Advertisement

A ranar 8 ga wata ne kotun ƙolin ƙasar da takatar da CBN daga wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar, bayan da jihohin uku suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar wa’adin.

 

Advertisement

To sai dai ministan shari’ar ƙasar, wanda shi ne ke wakiltar gwamnatin tarayya a shari’ar ya ce kotun ƙolin ba ta da hurumin shiga cikin lamarin.

 

Advertisement

Sannan kuma Malami ya ce masu shigar da ƙarar ba su sanya CBN cikin ƙarar ba.

 

Advertisement

Daga baya ne kuma jihohi bakwai suka shiga cikin jerin jihohin da ke goyon bayan jihohin uku, a yayin da johohi biyu suka mara wa gwamnatin taraya baya.

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending