Ana yin gumurzu tsakanin sojojin Sudan da rundunar tsaro ta musamman a Khartoum da wasu yankunan kasar, lamarin da ya jefa tsananin tsoro a zukatan ‘yan kasar.
A yau Asabar an ji karar manya-manyan bindigogi a sassa da dama na Khartoum, ciki har da tsakiyar birnin da Bahri da ke makwabtaka.
Hukumar NEMA Za’a Samu Ruwan Sama Mai Karfi A Abuja, Kano, Kaduna, Yobe, Bauchi Da Jigawa A Bana
A jerin sanarwar da ta fitar, rundunar tsaro ta musamman mai karfin iko, Rapid Support Forces (RSF), ta yi ikirarin kwace fadar shugaban kasar da wasu muhimman wurare.
Ta ce ta “kwace cikakken iko” na fadar shugaban kasar da filin jirgin saman Khartoum da na Merowe da ke arewacin kasar.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato rundunar sojin Sudan na cewa har yanzu ita ke da rike da dukkan sansanoninta da filayen jiragen sama.
Jiragen yakin Sudan sun kai hare-hare kan sansanonin RSF da ke Khartoum, a cewar rundunar sojin, inda ta karawa da cewa sojoji sun kai farmaki kan mayakan RSF kuma ta umarci fararen hula su zauna a gidajensu.
Kungiyar likitoci ta kasar ta ce kawo yanzu an kashe farar hula uku sakamakon arangamar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.
Tun da farko, an ji karar harbe-harben bindiga a kudancin Khartoum bayan an kwashe kwanaki ana zaman dar-dar tsakanin bangarorin biyu.
Suna tayar da jijiyoyin wuya ne game da wa’adin mika mulkin kasar ga gwamnatin farar hula.
Sai dai kafin nan shugaban mulkin soji na Sudan Janar Abdel Fattah al Burhan ya ce a shirye yake ya kawo karshen rashin jituwa tsakaninsu da RSF.
Wata sanarwa da masu shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu ce ta bayyana hakan ranar Asabar.
“Muna tabbatar wa jama’ar kasa cewa ana kan hanyar kawo karshen wannan rikici,” in ji sanarwar.
Zaman dar-dar ya karu tsakanin sojojin Sudan da RSF a ranar Alhamis bayan da rundunar ta mayar da sojojinta kusa da filin jirgin saman soji da ke birnin Merowe, abin da rundunar sojin kasar ta ce an yi shi ba tare da yardar ta ba.
Daga nan ne sojojin suka yi gargadi kan yiwuwar fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu.
Rundunar ta RSF, wadda tare da ita aka hada kai domin hambarar da gwamnatin Omar al Bashir a 2019, ta soma tura dakarunta zuwa Khartoum da wasu wurare a lokacin da ake tattaunawa a watan jiya kan mayar da rundunar cikin soji.
Wannan rashin jituwar tsakanin bangarorin biyu ya kawo jinkiri wurin saka hannu kan yarjejeniya ta karshe tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma kafa gwamnatin farar hula.
Bayan gargadin da sojin suka yi a ranar Alhamis, kungiyoyi da dama daga ciki da wajen Sudan suka fito domin shiga tsakani daga ciki har da ministan kudi na kasar Jibril Ibrahim da Gwamnan Darfur Minni Minawi da mamba a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Malik Agar.
Sauran sun hada da tsofaffin shugabannin ‘yan tawaye uku wadanda aka ba su mukami bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da su a 2020.
‘Babu kasa mai rundunar soji biyu’
Batun yin fito-na-fito da kuma yadda ake ganin motocin sulke da na soji a Khartoum ya sa jama’a suka shiga cikin zulumi, kamar yadda jama’a da dama suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Da dama sun dora alhakin hakan kan duka bangarorin biyu.
“Suna rikici kan mulki da jefa kasa cikin wani hali, mu kuma muna fafutukar samun abinci da abin sha da ilimi da kiwon lafiya,” in ji Nafisa Suleiman, yayin da take a wani wuri da ake sayar da kayan lambu.
“Ya kamata sojoji su rinka kare mutane amma a yanzu sun ne babbar barazana,” in ji wani mai shekara 35 Isam Hassan. “Ya kamata RSF ta zama karkashin soji. Babu kasar da ke da rundunar soji biyu,” kamar yadda ya kara da cewa.
