News
Wani Mutum Ya Kashe Mahaifiyarsa Kan Naira 10,000
DAGA ABDULKADIR MUHAMMADU TUKUNTAWA
Wani mutum da aka bayyana sunansa da Osaro Owate, ya shiga hannun hukumar ‘yansandan jihar Ribas bisa zargin kashe mahaifiyarsa a kauyen Alesa da ke karamar hukumar Eleme kan rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu kan naira dubu goma (N10,000) kacal.
Wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa ya na fama da matsalar gaulanci ko tsatstsauran ra’ayin addini na tsawon sama da shekara 30, ya amsa da bakinsa kan cewa ya kashe mamar tasa da fartanya ne.
Ma’aikatan N-Power Za Su Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana Kan Rashin Biyansu
Da yake magana ta cikin wani faifayin bidiyon da ya yadu sosai a Soshal Midiya, Owate ya ce, ya bukaci naira dubu ashirin (N20,000) a wajen marigayiyar mamar tasa domin ya sayi kayan sawa da zan yi adon zuwa wajen bisne wata gawa, amma sai ta ba shi naira 10 kacal, wanda kuma hakan ya sanyashi harzuka matuka.
Yace da naga ta hanani cikon ragowar kudin sai na bita har cikin kicin sa’ilin da take dafa abinci. na cigaba da rokonta kan ta bani cikon ragowar kudin. Amma duk da hakan ta cigaba da surfamin fada kawai sai na bugeta da fartanya. Tana kicin domin dafa abinci ne lokacin da na buga mata fartanya. lokacin na fusata matuka, kawai sai na gama da ita. Idan ni ma rayuwata za ta kawo karshe don na yi hakan ba damuwa na mutun kawai na shirya ma hakan. Ina fama da matsalar gaulanci sama da shekara 30. Kamar yadda kuke kallona yanzu ina son na mutum.”
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton rundunar ‘yansandan jihar Ribas ba ta fitar da wani bayani a kai ba.
