News
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Matashi Ɗan Shekaru 19 Da Miyagun Kwayoyi Sama Da Naira Miliyan 82 A Kano
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 19 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 82.7 a cikin birnin Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce kama wanda ake zargin ya biyo bayan sahihin bayani da jami’an tsaro suka samu daga masu ba da bayanai.
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Matashi Ɗan Shekaru 19 Da Miyagun Kwayoyi Na Naira Miliyan 82 A Kano
A cewar Kiyawa, a ranar 20 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, rundunar ta samu rahoto game da wata mota da ake zargin tana ɗauke da kwalaye cike da miyagun kwayoyi a unguwar Rimin Auzinawa cikin birnin Kano.
“Bayan samun rahoton, jami’an mu sun bi sahun motar har zuwa gidan da aka ajiye ta, inda suka kai samame suka kuma kama wani matashi mai suna Usman Umar, ɗan shekara 19, wanda ke zaune a gidan,” in ji sanarwar.
Binciken da aka gudanar a gidan ya kai ga gano miyagun kwayoyi kamar haka:
603 fakiti na Tramadol (kimanin 60,300 kwayoyi) – darajar su ta kai N60,300,000
299 fakiti na Pregabalin (kimanin 44,850 kwayoyi) – darajar su ta kai N22,425,00
Jimillar darajar miyagun kwayoyin da aka kama ta kai N82,725,000.
SP Kiyawa ya ce wanda ake zargin yana taimaka wa jami’an tsaro wajen gano sauran mambobin ƙungiyar da ke da hannu a safarar miyagun kwayoyin, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai hare-hare da sintiri a sassa daban-daban na jihar domin dakile safarar miyagun kwayoyi da sauran laifuffuka masu nasaba da su.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
