Connect with us

News

Wani mutum Ya Yi Dambe Da ’Yan Bindiga Ya Kwaci Mahaifinsa A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Wani da ’yan bindiga suka kai hari gidansu da nufin yin garkuwa da mahaifinsa a Jihar Kano ya yi dambe da su, ya kwaci mahaifin nasa.

Advertisement

 

Masu garkuwa da mutanen sun yi kutse ne a gidan wani magidanci da ke kauyen Yarimawa da ke Karamar Hukumar Tofa ta jihar ne da nufin sace shi da dansa, amma suka gamu da gamonsu, inda dan nasa ya turje, lamarin ya fara dambe da su.

Advertisement

Ƙungiyar Likitocin kasar nan za ta shiga yajin aiki

Dan mutumin yana cikin dambe da ’yan bindigar ne sauran suka yi yunkurin su harbe shi, amma suka yi kuskure, suka dirka wa abokinsu harbi, ya mutu nan take.

 

Advertisement

 

Jaridar aminiya ta rawaito cewa Da yake gabatar da su bayan an kamo su, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel, ya ce, “Magidancin ya tsare, amma a kokarin maharan na kama dansa, sun harbi wasu mutum biyu da suka kawo dauki a kafa.

Advertisement

 

“An kai wadanda aka harba din Babban Asibitin Tofa domin ba su kulawa kuma har an sallame su.”

Advertisement

 

Ya ce daga baya da aka gudanar da bincike aka kamo mutum hudu da suka yi yunkurin yin garkuwa da mutanen.

Advertisement

 

Wadana ake zargin sun shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar cewa wani na kusa da iyalan magidancin ne ya tura su su yi garkuwa da shi da dansa.

Advertisement

 

Daya daga cikinsu ya ce, “Mun je gidan yadda aka ba mu umarni, amma dan mutumin ya turje, a garin harbin sa ne muka dirka wa abokinmu harbi. Amma ni ban ban taba yi ba, wannan ne na farko, kuma na yi nadama.”

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending