News
Ƙungiyar Likitocin kasar nan za ta shiga yajin aiki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta kasa ta ayyana shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyar kan gaza biya mata buƙatunta da gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi.
Ƙungiyar ta bayyana ɗaukar matakin ne bayan ganawar da shugabanin kwamitin gudanarwarta ya yi ranar Litinin.
Likitocin sun ce za su fara yajin aikin gargaɗin ne daga ranar Laraba 17 ga watan Mayu zuwa ranar Litinin 22 ga wata.
Likitocin na buƙatar gwamnati ta gaggauta yin ƙari a tsarin albashin ɓangaren lafiyar ƙasar da kashi 200 kan albashin likitocin na yanzu.
Sannan a ƙara musu kuɗin alawus da suka nema cikin wata wasiƙa da shugaban ƙungiyar ya rubuta wa ministan lafiyar ƙasar Dakta Osagie Ehanire ranar 7 ga watan Yulin 2022.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta biyan su kuɗin horaswa na shekarar 2023, kamar yadda yake ƙunshe cikin yarjejeniyar da suka cimma a wata ganawa da masu ruwa da tsaki, da ma’aikatar lafiyar ƙasar ta jagoranta.
Sannan kuma ƙungiyar na buƙatar gwamnatin tarayya da ta fara biyan wasu mambobinta bashin albashin da suke binta a shekarun 2014 da 2015 da kuma 2016.
A ranar 29 ga watan Afrilu ne dai ƙungiyar likitocin ta bai wa gwamnatin tarayyar ƙasar wa’adin mako biyu da ta zartar da yarjejeniyar da suka cimma ko kuma ta tsunduma yajin aiki
