Connect with us

News

Saudiyya da Amurka sun yi maraba da tsawaita yarjejeniyar Sudan

Published

on

Amurka da Saudiyya sun yi maraba da tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da dakarun kar-ta-kwana na RSF da kwana biyar.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen biyu masu shiga tsakani a rikicin sun amince cewa yarjejeniyar farko da aka cimma ta kasance ta je-ka-na-yi-ka, to amma duk da haka ta bayar da damar shigar da kayan agaji ga miliyoyin mutane a Sudan din.

Advertisement

Abba Kabir Ya Rushe Shugabannin Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano Tare Da Nada Sabbi

Shirin samar da abinci na duniya, ya ce a karon farko ya samu damar aikewa da abinci ga mutanen da suka makale a babban birnin kasar, Khartoum, tun bayan fara yaki a Sudan din.

Rikicin da aka fara tsakanin bangarorin biyu a kan gwagwarmayar kama iko tun wajen mako shida ya tilasta wa jama’a da dama ficewa daga kasar musamman babban birnin sannan ya jefa da dama cikin mawuyacin hali.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending