News
Bikin Rantsar da Sabbin Kwamishinonin jihar Jigawa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A Namadi ya jagoranci rantsar da sabbin Kwamishinonin sa guda goma sha shida da ya naɗa.
An gudanar da taron rantsuwar ne a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
An Samu Raguwar Hatsarin Mota da ake fuskanta a yayin Babbar Sallar bana.– FRSC
Sabbin kwamishinonin sun hada da:
1. Hon Sagir Musa Ahmad a matsayin kwamishinan Yada Labarai, Matasa da Wasanni da kuma Al adu.
2. Hon Garba Ahmad Kwamishinan Kananan Hukumomi.
3. Hon Hadiza Abdulwahab Kwamishiniyar Harkokin Mata.
4. Hon Aminu Kanta kwamishinan Kasuwanci.
5. Dr Nura Ibrahim Dan Doka Kwamishinan Muhalli.
6. Hon Ibrahim Giwa Kwamishinan Ruwa.
7. Dr Muhammad Kainuwa Kwamishinan Lafiya.
8. Dr Lawan Yunusa Danzomo Kwamishinan Ilimi.
9. Hon Ibrahim B Umar Kwamishinan Kasafi da tsare tsare.
10. Dr Yusif Ahmad Chamo Kwamishinan Ilimi mai Zurfi.
11. Farfesa Hannatu Muhammad Kwamishiniyar a Ma’aikatar kudi.
12. Engr Gambo Shuaibu Kwamishinan Ayyuka.
13. Kanal Muhammad Alhassan Kwamishinan Raya Kasa.
14. Hon Muttaka Namadi Kwamishinan Noma.
15. Hon Musa Adamu Aliyu Kwamishinan Shari’a.
16. Hon Auwal D Sankara Kwamishinan Ayyuka na Musamman.
Gwamna Umar Namadi ya bukaci sabbin Kwamishinan su kasance masu gaskiya da rikon amana, sannan su taimaka masa wajen cimma manufofin gwamnatin sa.
