News
Sojojin Nijar Sun Gargadi ECOWAS Kan Amfani Da Karfi Wajen Dawo Da Mulkin Farar Hula
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Shugabannin Sojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun gargadi shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da su kauce wa duk wani shiri na tura sojoji kasarsu da zummar mayar da tsohuwar gwamnatin da suka kawar daga karagar mulki.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijar, Janar Abdourahmane ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, inda Mohamed Bazoum ke hannun sojoji tun bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya.
Yau Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Fara Tantance Ministoci.
A karshe kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta ba da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin mulkin soja a Nijar da ta maida shugaba Bazoum kan mukaminsa ko kuma su fuskanci tsauraran takunkumi.
Da suke mayar da martani, shugabannin sojoji a Nijar sun yi gargadi kan duk wani matakin soji a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar ta Nijar.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
