News
Hukumar NECO tace mutum miliyan 1.2 suka yi rijistar zana jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2023
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta sanya adadin wadanda suka yi rijistar zana jarrabawar kammala sakandare na shekarar 2023 da ke gudana a kan mutane miliyan daya da dubu dari biyu da biyar da dari takwas da tamanin da takwas, (1,205,888).
Shugaban Hukumar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana hakan a Jihar Filato ranar Juma’a, yayin da yake sa ido kan yadda ake gudanar da jarabawar a wasu makarantu.
Gwamnan jihar Adamawa ya naɗa mutum 47 a matsayin masu taimaka masa a fannin yaɗa labarai .
Farfesa Wushishi wanda ya yi magana ta hannun sashin yada labarai da hulda da jama’a na HOD Azeez Sani, ya bayyana cewa a cikin wannan adadi mutane 601,074 maza ne yayin da 584,814 mata ne.
Ya bayyana jin dadinsa da yadda ake gudanar da babban taron SSCE na 2023 bisa rahotannin da aka samu daga sassan kasar nan.
Magatakardar ya kuma lura cewa 2023 SSCE da za a kammala mako mai zuwa ita ce mafi kyawun tsari a cikin ‘yan shekarun nan.
Farfesa Wushishi ya bayyana cewa an dauki matakai daban-daban na duba kura-kuran jarabawar, inda ya kara da cewa matakan sun fara samun sakamako mai kyau.
Magatakardar da ya sa ido a jarabawar a makarantar Soja ta Airforce; King and Queens Academy da Emmanuel International College duk a Jos, sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da jarabawar a makarantun da suka ziyarta.
Tun da farko Farfesa Wushishi ya sanya ido kan yadda 2023 SSCE ke gudana a jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa da Bauchi.
