News
jami’ar Chicago: Martanin Atiku Da Obi Kan Rahoton BBC Na Rashin Samun Hujjar Zargin Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsagin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaran sa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun nuna rashin amincewarsu da rahoton BBC ta fitar na cewa babu wata shaida da ke tabbatar da zargin jabun takardun karatu da ake yiwa shugaba Bola Ahamad Tinubu.
Tawagar BBC a wani rahoton binciken tantance gaskiyar labari da aka wallafa ranar Laraba ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa Tinubu ya yi karya a takardar shaidar jami’ar Jihar Chicago da ya mika wa INEC.
Dole ne Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu Subi ƙa’idoji – Prof. Salisu
Da yake mayar da martani, mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga Atiku Abubakar, Phrank Shaibu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rahoton na BBC a matsayin wani bangare na shirin farfaganda na gwamnatin Tinubu.
Su kuwa shugabancin jam’iyyar Labour ta bakin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar, Kehinde Edun, ya ce rahoton da kafar yada labarai ta Burtaniya ta fitar bai girgiza su ba, wanda suka yi nuni da cewa yunkuri ne na kawar da labarin zargin da ake yiwa shugaban kasar.
Wani labarin kuma Dole ne Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu Subi ƙa’idoji – Prof. Salisu
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
