News
Shugaban Kungiyar Hamas Ta Zargi Israila Da Aikata Kisan Kiyashi A Gaza
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Kungiyar Hamas ta Falasdinawa Ismail Haniyeh ya zargi kasar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a yakin da take yi a zirin Gaza, a kokarin na yin ramuwar gaiyya.
Shugaban kungiyar ya zargi Isra’ila da aikata lefin kisan ‘kare dangi akan fararen hular da babu ruwansu a yakin da ake gwabzawa.
Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta buƙaci a ɗauki shugabanta, Ajaero zuwa ƙetare don yi masa magani
A jawabin da ya gabatar, shugaban kungiyar Hamas ya yi alkawarin cewar lefukan da Isra’ila ke aikatawa ba zai kubutar da ita daga galabar da aka samu akan tab a.
Hakan na zuwa ne a yayin da a karon farko motocin daukar marassa lafiya daga Gaza dauke da falasdinawa suka cikin masar ta kan iyakar Rafah domin nemar masu magani.
A wani labarin kuma Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta buƙaci a ɗauki shugabanta, Ajaero zuwa ƙetare don yi masa magani
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
