Connect with us

News

Babban Bankin Kasa CBN Ya Musanta Rahotannin Karancin Kudade A Bankuna

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Babban bankin Najeriya CBN ya musanta rahotannin da ke cewa ana fama da karancin kudi a bankuna, injinan cirar kudi na ATM, wuraren POS, da kuma kasuwar canjin kudade a wasu manyan biranen kasar.

Daraktan Sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin ne ya musanta rahoton a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Advertisement

Shugaban Kungiyar Hamas Ta Zargi Israila Da Aikata Kisan Kiyashi A Gaza

AbdulMumin ya ce ana ganin karancin kudi a wasu wurare na faruwa ne saboda yawan kudaden da ake cirewa daga rassan bankin CBN ta bankunan ajiya da kuma turuwar da kwastomomi ke yi wajen cire kudi daga na’urar ATM.

 

Advertisement

“Yayin da muka lura da damuwar ‘yan Najeriya kan yadda ake samun tsabar kudi domin hada-hadar kudi, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun takardun kudi na ayyukan tattalin arziki a kasar nan.

“Sassan bankin na CBN a fadin kasar nan kuma suna aiki don tabbatar da cewa an samu raguwar kudaden a jihohinsu na aiki,” inji shi

Advertisement

Don haka ya bukaci jama’a da su kiyaye kada a firgice saboda akwai isassun jari don saukaka harkokin tattalin arziki.

 

Advertisement

“An kuma shawarci ‘yan Najeriya da su rungumi wasu hanyoyin biyan kudi, wanda zai rage matsin lamba kan amfani da tsabar kudi,” in ji shi.

A wani labarin kuma Shugaban Kungiyar Hamas Ta Zargi Israila Da Aikata Kisan Kiyashi A Gaza

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending