Connect with us

News

Hatsarin Kwalekwale Ya Yi Ajalin Mutum 10 A Jihar Neja

Published

on

DAGA AMINU AHMAD FULATAN 

 

Advertisement

Akalla mutum 10 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kifewar kwalekwale da yammacin Alhamis a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 4:00 na yammacin Alhamis.

Advertisement

Yadda CBN Ya Karya Darajar Naira  – Sanusi

Hatsarin dai ya ritsa da mutanen ne, wadanda galibinsu ’yan kasuwa ne da ke kokarin kai kaya daga kauyen Zongoru na gundumar Bass, a kan hanyarsu ta zuwa Gijiwa, domin shirin cin kasuwar Kuta, hedkwatar Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar.

Bayanai sun ce mutum 32 ne a cikin jirgin lokacin da ya kife, inda mutum 10 suka mutu, 22 kuma masunta suka ceto su da ransu.

Advertisement

Saidu Salihu, Sakataren kungiyar ci gaban Shiriro, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Aminiya, inda ya ce tara daga cikin wadanda suka rasu tara mata ne, daya kuma namiji.

Aminiya ta ruwaito cewa  duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Advertisement

A wani labarin kuma Yadda CBN Ya Karya Darajar Naira  – Sanusi

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Isra’la da ta kawo ƙarshen ayyukan sojinta da ke yi kan Hamas tare da kiran gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Advertisement

Mista Erdogan ya yi wannan kira ne a lokacin taron manema labarai da ya gabatar tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a lokacin da ya kai ziyara Jamus.

Shugaban na Turkiyya ya ce ya kamata Jamus ta yi aiki da Turkiyya domin tabbatar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

Advertisement

Erdogan – wanda ya kira Hamas da “masu ƙwatar ‘yanci” – ya ce laifin da ake jin an aikata na kisan kiyashin ‘Holocaust’ da aka yi wa Yahuwada wanda Turkiya ta goyi baya, ba zai zame mata dabaibayi ba., yana mayar da martani kan goyon bayan da Jamus ke bai wa Isra’ila.

A nasa ɓangare Mista Scholz ya ce Jamus ba za ta yi sassauci kan ‘yancin Isra’ila na rayuwa da kare kanta ba.

Advertisement

Shugabannin biyu sun amince da shirya muhimmiyar tattaunawa kan yadda ƙasashensu za su taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending