News
Yadda CBN Ya Karya Darajar Naira – Sanusi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi ya bayyana yadda babban bankin Nijeriya (CBN) ya karya darajar naira.
Sanusi ya bayyana cewa, ba da lamuni da CBN ya bai wa gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hanyoyi daban-daban, ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, wanda ya kai ga faduwar darajar naira.
Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wurin taron kasuwanci na MTN a ranar Talata. Sanusi ya yi nuni da cewa, CBN ya tsunduma cikin matsananciyar karancin kudade ta hanyar amfani da wasu matakai daban-daban, da suka hada da bude kasuwannin harkokin kudade, da OBB da kuma haraji.
Ya bayyana cewa, wadannan matakan sun nuna yadda babban bankin ya jajirce wajen gudanar da ayyukansa na tabbatar da daidaiton tsarin hada-hadar kudi da kuma shawo kan hauhawar farashin kayayyaki.
“Ina da kyakkyawan fata, musamman a cikin gajeren lokaci abubuwa za su daidaita. Mun sami shekara takwas ba tare da daidaita abubuwa ba a babban bankin Nijeriya.
A wani labarin kuma Ba Nu Sami Wani Dalilin Da Za A Ce Shirin AGILE Ya Sabawa Addini, Da Al’adu Aa Kuma Zamantakewar Mu – Gamayyar kungiyoyi
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen Laberiya, Joseph Boakai na ci gaba da zama kan gaba yayin da hukumar zaɓen ke ci gaba da ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar.
Kawo yanzu mista Boakai – wanda tsohon shugaban ƙasar ne, mai shekara 64 – ya samu kashi 50.89 na ƙuri’un da aka kaɗa bayan kammala ƙidaya kashi 99.58 a ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da shi kuma shugaban ƙasar George Weah ke sa kashi 49.11.
Shugabar hukumar zaɓen ƙasar, Davidetta Lansanah, ta ce za a sake zaɓen a wasu rumfuna 25 kafin a bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen.
Ƙanƙanin rinjaye kawai ɗan takara ke buƙata kafin lashe zaɓen.
Shugaba Weah na buƙatar ƙarin lokacin shugabanci, domin inganta harkokin ilimi, da magance rashin aikin yi da cin hanci da rashawa.
Yayin da shi kuma Mista Boakai ya alƙawarta ceto Laberiya daga abin da ya kira ”rashin iya shugabancin Weah da ya yi almabazzaranci da dukiyar ƙasar”
