News
Bamu Sami Wani Dalilin Da Za a Ce Shirin AGIlLE Ya Sabawa Addini Da Al”adu Da Zamantakewa Ba – Gamayyar kungiyoyi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gamayyar wasu kungiyoyi guda 11 dake jihar kano sun ce Sunbi diddigi tare da tuntubar wadanda Shirin AGILE ya shafa a jihar Kano don ganu maganganu da wasu ke yi na muzanta ga shirin, kuma sun gano wadancan labarai ba su da tushe ballantana makama.
Gamayyar kungiyoyin sun ce sun bibiya wadanda abun ya shafa musamman gwamnati da jami’an shirin, da wasu daga cikin iyayen yaran sama da 800,000 dake makarantun gwamnati a jihar Kano, da su kansu daliban, da malaman da ke ba da horon, da sauran masu ruwa da tsaki, Haka kuma sun bibiyi ita kanta manhajar da ake horar da yaran, tare da sauran manhajojin sauran darussan sakandire, ba mu sami wani dalili da za a ce Shirin ya sabawa Addini, da al’adu da kuma zamantakewarmu, amma bamu samu ba .
Gobara Ta Kone Kasuwar Kifi, Ta Lalata Dukiyar da Ta Kai N120m A Legos
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren gamayyar kungiyoyin Amb. Nura Abdullahi Saraki ya sanyawa hannu kuma aka aikowa da jaridar Inda Ranka.
“Don haka wannan batu kage ne mara tushe da muka kasa gane abinda masu yada shi ke burin cimma, sabanin cigaban al’ummar Jihar Kano baki daya.
A zurfafa bincikenmu, mun tabbatar cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da shirin AGILE tun shekarar 2021, tare da jihohin Bomo, Katsina, Kaduna, Kebbi, Plateau da Ekiti”. A cewar sanarwar
“Kuma saboda alfanin shirin a yanzu haka wasu karin jihohi sun sami nasarar shiga. Kamar Jigawa, Zamfara, Bauchi, Gombe, Yohe, Kogi, Niger, Kwara da sauransu. Rawar da Bankin
Duniya ke takawa kawai ita ce shine ya ba da lamanin kudaden gudanarwa, wanda kurna za a biya cikin wasu shekaru nan gaba”.
” Mun bincika kuma mun tabbatar shirin AGILE ba shi da wata alaka ta kusa ko ta nesa da Yahudawaba kamar yadda zuzuta hakan, a Fili ko a boye. Kuma dukkan al’umma suna ganin irin alfanun da wannan shiri ya kawo a
makarantun sakandire na duk fadin Jihar Kano”. Inji gamayyar kungiyoyin
Wannan kungiya tamu tana kira ga dukkan jama’a da su bibiyi makarantun yankunansu, iyaye kuma su tuntubi ‘ya’yayensu, do min tabbatar da sahihiyar gaskiyar lamarin.
Kuma sun ce kofar jami’an wannan shiri, da ta mahukunta a bude take ko da yaushe, ga masu neman karin bayani, ko shawara, ko tattaunawa game da dukkan tsare-tsaren wannan shiri, a ofishinsu da ke hawa na uku, Gidan Murtala, Kofar Nassarawa, cikin Birnin Kano.
“Muna shawartar al’umma da muguji yada jita -jita ba tare da bincike a kan ingancin labarurrukan yanar gizo ba, musamman game da muhimmin kokari da Ma’aikatar Ilmi ke yi wajen inganta rayuwar al’umma domin ci gaban Jihar Kano baki daya”.
Ga sunayen Gamayyar kungiyoyin jahar Kano masu fafutukar samar daci gaban da suka gudanar da binciken.
-Network For Youth Enlightenment And Development N-YED,
-Association of Nigerian Women and Youths for Peace Advocates
(ANWOPA) Kano chapter, Youth
-Mobilization by Media,
-Fighting Against —
•Women and Children Violation, Kano
Youth Progressive Concern,
-Arewa Peace Ambassadors,
-NACCRAN Kano State,
-Arewa Youth Innovative of Nigeria.
Kano Progressive Mindset Forum.
Kano State Network for youth Initiative.
Arewa Youths Political Gladiators (AYPG),
-Kainuwa Youth Progressive Community Development.
-African Emancipation Movement (Kano Chapter),
Arewa Students Forum,
-Daliban Nigeria Reshan jahar Kano
-KASYADREC ( DRUGS ORG.)
