News
Gobara Ta Kone Kasuwar Kifi, Ta Lalata Dukiyar da Ta Kai N120m A Legos
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gobara ta kone sashen hannun jari na shahararriyar kasuwar kifi ta Oyingbo tare da lalata wasu kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 120.
Ziyarar da jaridar Vanguard ta kai wurin da lamarin ya faru ya nuna cewa kimanin shaguna bakwai da suke cike makil da kifin sun zama toka ina wasu kayayyakin suke watse a kasuwar.
Ma’aikatar Lafiya da Asibitin Kashi na Dala za su Hada Hannu Wajen Horar da Ma’aikata
Duk da cewa majiyar mu ta kasa gano musabbabin tashin gobarar, sai dai ‘yan kasuwar da suka zanta da wakilinmu sun ce gobarar ta tashi ne bayan tsakar dare amma an kashe gobarar bayan shafe sama da sa’o’i biyu ana gwabzawa domin shawo kan lamarin.
Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin masu shagunan da lamarin ya shafa Mista Davidson Okenwa ya ce ya samu waya da misalin karfe 12:30 na safe cewa kasuwar ta na cin wuta kuma shagunan sa hudu abin ya shafa.
Okenwa ya kuma ce gaba daya shagunan sa guda bakwai sun kone tare da wawashewa yayin da gobarar ta lalata kayayyakin da suka kai sama da Naira miliyan 70.
Ya ce: “Da misalin karfe 12:20 na safiyar yau, na samu kiran waya daga wannan kasuwa, sai na garzaya daga gidana da ke Ijegun inda na samu gano cewa shagunana hudu sun kone gaba daya yayin da wasu kuma aka yi awon gaba da su.
“Ina cikin halin kunci domin na dauki wani gini daga bankin First City Monument, FCMB. Ni gaba ɗaya na rasa abin da zan yi. Adadin kifin da gobarar ta lalata ya haura Naira miliyan 70 domin na kai kayan ne kwana daya kacal kafin aukuwar gobarar.”
Da yake magana kan wannan ci gaban, Greg Ilobinso, wani babban dillali ne a harkar hada-hadar kifin da ke yankin Gabas, ya ce ana bukatar samar da tashar kashe gobara a kasuwar dan mayar da martanin gaggawa idan irin hakan ta afku saboda ana hasarar miliyoyin Nairori.
Ilobinso ya kuma ce har sai gwamnatin Legas ta ga bukatar kare rayuka da dukiyoyi a wannan kasuwa, gwamnati da ‘yan kasuwa za su ci gaba da asara.
Ilobinso ya yi kira ga kamfanonin inshora da su fito da kayayyakin inshorar kasuwar da nufin rage asarar da aka samu a irin wannan yanayi.
“Wasu abokan cinikina ne suka sanar da ni halin da ake ciki a safiyar yau, kuma ina raba radadin ’yan kasuwar da shagunansu ya shafa, kuma ina fatan gwamnatin Jihar Legas da ta ke da girma ta taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da jin illar asarar da aka yi na masu shagunan da abin ya shafa.
A wani labarin kuma Ma’aikatar Lafiya da Asibitin Kashi na Dala za su Hada Hannu Wajen Horar da Ma’aikata
Shirin samar da abinci na duniya WFP ya ce al’ummar Gaza miliyan biyu na buƙatar agajin abinci cikin gaggawa, tare da yin gargaɗin cewa fararen hula na fuskantar barazanar faɗa wa yunwa.
Babu gidajen biredi na WFP da ke aiki a yanzu saboda ƙarancin man fetur, kuma kantunan sayar da abinci kaɗan ne ke buɗe, a cewar shirin.
Ya ce abinci ɗan kadan ne ake da shi a kantunan kuma farashinsa ya tashi sama.
Rashin man fetur da wutar lantarki na nufin cewa yin garki ya zama da wuya ga iyalai da yawa.
Kaɗan ne ke samun damar cin abinci, inda wasu ke rayuwa kan kowane irin abu suka samu, in ji WFP.
