Connect with us

News

Kotu Ta Daure Wani Jigon Jam’iyyar APC A Jihar Legas Saboda Laifin Sayen Kuri’u A Zaben 2023

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Wata babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta yanke wa wani shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Surulere, Wahab Hammed hukuncin daurin shekara daya a gidan yari.

Mai shari’a Ismail Ijelu ya yanke wa wanda ake kara hukuncin ne bisa laifin siyan kuri’u bayan ya same shi da laifuka biyu da suka hada da hada baki da cin hanci.

Advertisement

Anyi kira ga yan majalisar jihar kano da kada su bar abba kabir ya tafi hutu -Ahmad s aruwa 

Lauyan hukumar EFCC, Samuel Daji, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda ake tuhuma ya hada baki da wani Segun Ijitola wanda har yanzu bai je gaban kotun ba, wajen aikata cin hanci da rashawa da masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Ijelu ya yanke wa Hammed hukuncin daurin shekara daya ko kuma tarar Naira milliyan 1.

Advertisement

A wani labarin kuma Anyi kira ga yan majalisar jihar kano da kada su bar abba kabir ya tafi hutu -Ahmad s aruwa 

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending