News
Dr. Labaran ya bayar da tabbacin aiwatar da tsarin kundin manufofin habaka lafiya.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf a shirye take ta aiwatar da kundin manufofin habaka lafiya bayar yi masa gyare-gyaren da za su dace da jihar Kano.
Kwamishinan ya baiyana wannan batu ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na kwanaki 3 na fitar da tsarin da zai aiwatar da manufofin kundin habaka harkokin lafiya samar a jihar Kano, wanda aka gudanar a jihar Kaduna.
Da Ɗuminsa: Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa Nnamdi Kanu
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami in yada labarai Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Dr. Labaran ya ce, Alhaji Abba Kabir Yusuf yana da kundin manufofin da zai aiwatar a jihar Kano tun lokacin da ya fito takarar neman kujerar gwamnan jihar tare da bayar da hankali ta musamman ga harkokin kiwon lafiya, yana mai jaddada cewa duk wani shiri da zai dace da abubuwan da kundin ke dauke da shi ba shakka zai samu cikakken goyon baya da amincewar Gwamnan
Ya yi nuni da cewa samun kudaden aiwatar da ayyuka abu ne mai sauki a wajen gwamnati mai ci, yana mai jaddada cewa abin kawai da ake bukata shi ne manajoji masu aiwatar da shirye-shirye su yi bayani mai gamsarwa sannan su bibiyi abin har sai ya tabbata.
Daga nan sai Kwamishinan ya bukaci mahalarta taron da su yi aiki tukuru domin samar da ingantaccen kundi bisa la’akari da bukatun jihar Kano, yana mai ba da tabbacin cewa zai kai wa Gwamna don neman sahalewarsa da nufin cimma burin muradun harkokin kiwon lafiya na duniya.
Shi ma da yake jawabi, Darakta mai kula da Lafiyar Al’umma da Dakile Yaduwar Cututtuka na Ma’aikatar, Dr. Ashiru Rajab, ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa cewa za a maye gurbin Jami’ai Masu Fadakarwa a kan Lafiya idan aka kammala aiwatar da kundin manufofin habaka lafiya.
Dr. Rajab ya ce abin da jihar Kano ke da shi shi ne ilimin fadakarwa kan lafiya, a daidai lokacin da, a matakin duniya, kasashe sun canja daga ilimin fadakarwa kan kiwon lafiya zuwa ilimin habaka kiwon lafiya domin samun ingantattun ayyukan bunkasa lafiya a duniya.
Ya bayyana cewa Najeriya, a matsayinta na kasa, ta shiga sahun sauran kasashen don canjawa daga ilimin fadakarwa kan lafiya zuwa ilimin habaka kiwon lafiya, inda ya kara da cewa Kano na daya daga cikin jihohin kasar nan da ke daukar matakan kawo wannan sauyi don tabbatar da cewa ita ma ta sauya zuwa shirin inganta kiwon lafiya.
Daraktan ya jaddada cewa muhimmancin haka shi ne ilimin inganta kiwon lafiya ya fi fadi wanda ke ba da damar shigo da masu ruwa da tsaki masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da kuma tabbatar da walwalar al’ummar jihar Kano.
Dr. Rajab daga nan sai Rajab ya tabbatar wa jami’in da ke fadakarwa a kan kiwon lafiya da ke aiki a matakin jiha da karamar hukuma da kuma shiyya cewa jita-jitar ba gaskiya ba ce, hasali ma ma’aikatar ta yi mamakin daga ina ta samo asali, inda ya tabbatar da cewa abin da jihar ke yi shi ne tabbatar da cewa gaba dayansu an ba su damar cike gibin ilimin da suke da shi ta hanyar ƙarin kwasa-kwasai a fannin ilimin habaka lafiya, sannan kuma za su ci gaba da aikin su kamar yadda suka saba.
Ya kara da cewa babu daya daga cikinsu da za a maye gurbinsa, kuma dukkansu ma’aikatar lafiya za ta tallafa musu domin cike wannan gibin, yana mai jaddada cewa da dimbin gogewar da suke da ita a matsayinsu na jami’ai masu fadakarwa kan kiwon lafiya, zai yi musu sauki su ci gaba da aiki a matsayin jami’an inganta kiwon lafiya.
Wanda ya samu cikakken tallafi daga FCDO-Lafiya, manufofin taron sun hada da bayyana wa masu ruwa da tsaki na jihar cikakken bayani game da Shirin Habaka Lafiya (NPHH) na Kasa na 2019 da aka yi wa kwaskwarima sake da kuma fitar da hanyar da za a yi amfani da ita wajen sauya wasu abubuwan da kundin na NPHH 2019 ke dauke da su da za su dace da samar da jihar Kano.
Sauran manufofin su ne samar da matakan da za a bi domin aiwatar da matsayar da jihar Kano ta dauka na rungumar tsarin NPHH na 2019 bisa la’akari da sakamakon binciken da aka yi na tantance karfin inganta kiwon lafiya a matakin jiha da karamar hukuma a jihar Kano, da kuma kafa wata kwamitin kwararru na mutane 12 kan ilimin habaka (TWG-HP (da nufin rikidewa zuwa wata Rumfa ta ta Ilimin Habaka Lafiya) da zai tabbatar da cewa an lalubo dukkan abubuwan da suka dace da su kai ga samun nasarar aiwatar da shirin a fadin jihar Kano.
