News
Yajin Aikin NLC:Maganar soma yajin aiki ranar Litinin ƙarya ce – Nlc
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da sanarwar yajin aikin da ake zargin ta shirya yi a ranar Litinin.
Benson Upah, shugaban yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta koma saman teburin firimiya bayan doke Brighton
Akwai wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar ta NLC da kuma babban sakataren kungiyar ta TUC, Emmanuel Ugboaja, da Nuhu Toro, dake cewa za a fara yajin aikin a fadin Najeriya ranar Litinin.
Premium Times ta cewa A cewar Upa, maganar karya ce kuma babu sanarwar yajin aiki daga gare su.
“Muna so mu sake tabbatar wa Ƴan Najeriya cewa wannan sanarwar ba ta fito daga gare mu ba, kuma ba mu da niyyar fara wani yajin aiki a wannan lokacin,” in ji shi.
Ya ce an shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da hidimomin su yi watsi da sanarwar su dauke shi a matsayin na karya kawai.
A wani labarin kuma Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta koma saman teburin firimiya bayan doke Brighton
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
