Connect with us

News

Wani Mutum Ya Hallaka Magatakardar Kotu da Aka Aika Masa Domin Ya ya Gayyace Shi Zuwa Kotu.

Published

on

Linus Dimas

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wani mutum a jihar Adamawa mai suna Linus Dimas ya kashe magatakardar kotu da aka aika masa domin ya gayyace shi zuwa kotu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a yammacin ranar Talata, inda ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargin a ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, a lokacin da ake zargin ya kashe magatakardar Kotu da ya je ya Kai masa takardar sammacin kotu.

Advertisement

Hausawan Jihar Ogun Na Zanga-zangar Neman Tabbatar Da Adalci A Shari’ar Gwamnan Kano

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Suleiman Nguroje, ta ce Linus Dimas mai shekaru 43, mazaunin Kugama Wuro Jibir ne a karamar hukumar Mayo Belwa.

Daily Post ta ruwaito cewar sanarwar: “Wanda ake zargin, a ranar 18 ga watan Disamba, 2023, ya ki amincewa da sammacin kotu da Yauba Usman, magatakardar kotun yankin Nasarawo Jereng ya Kai masa inda wadanda Ake Zargin suka kai masa hari tare da daba masa wuka da dama, wanda hakan ya yi masa rauni sosai.”

Advertisement

A wani labarin kuma Hausawan Jihar Ogun Na Zanga-zangar Neman Tabbatar Da Adalci A Shari’ar Gwamnan Kano

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending