Connect with us

News

Hausawan Jihar Ogun Na Zanga-zangar Neman Tabbatar Da Adalci A Shari’ar Gwamnan Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Al’ummar Hausawa da mazauna garin Sagamu da ke jihar Ogun da dama ne suka fito suna gudanar da zanga-zangar lumana domin neman a yi adalci kan hukuncin zaben gwamnan Jihar Kano da ke gaban kotun koli.

‘Yan Arewa masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne da kananan yara, sun bi manyan titunan garin Sagamu, suna rera wakokin hadin kai tare da yin kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sa baki a lamarin don dakile zargin kulla makarkashiyar karya doka da oda a fadin Nijeriya.

Advertisement

An gurfanar da wasu manoma shida bisa zargin kashe makiyayi da shanun sa 97 a Jihar Kano

‘Yan Arewa mazauna garin Sagamu dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban, sun bayyana fargabar cewa rikicin Kano na iya yaduwa zuwa Kudancin kasar nan idan har bangaren shari’a ya yi amfani da duk wata dabarar da za ta bi wajen tabbatar da sabanin abun da masu kada kuri’a a Jihar Kano suka zaba wanda aka bayyana a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a zaben gwamna a jihar.

Leadership ta ruwaito cewa Sun yi kira da a yi adalci da zai kawo zaman lafiya, sun kuma yi gargadin cewa zaman lafiya na iya karanci a Nijeriya idan ba a yi abun da ya dace kan lamarin shari’ar ta Kano ba.

Advertisement

Wasu daga cikin rubuce-rubucen da aka rubuta a allunansu an rubuta: “Ka guji zubar da jini, a tabbatar da zaman lafiya a Kano”; “Muna zaune a kudu lafiya, amma rashin adalci a Kano na iya yada tashin hankali”; “Matsalar Kano na iya yaduwa zuwa Kudu”; “A yi adalci don samun zaman lafiya a Kano” da sauransu.

A wani labarin kuma An gurfanar da wasu manoma shida bisa zargin kashe makiyayi da shanun sa 97 a Jihar Kano

Advertisement

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Advertisement

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Advertisement

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Advertisement

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending