Connect with us

News

An gurfanar da wasu manoma shida bisa zargin kashe makiyayi da shanun sa 97 a Jihar Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Noman’s Lands a jihar Kano ta bayar da umarnin garkame wasu manoma shida bisa zarginsu da hannu wajen kashe wani makiyayi da shanu 97 a karamar hukumar Bagwai ta jihar.

Alkalin kotun, Talatu Makama, a ranar Litinin din da ta gabata ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa ranar Laraba domin sauraron karar.

Advertisement

An Samu Rahoton Tashin Gobara A Jahar Kaduna Sau 33 Cikin Watan Nuwamba 

Wadanda ake zargin a cewar rahoton farko na ‘yan sanda (FIR) sun hada da Sani Abdullahi, Ilyasu Isa, Saleh Saidu, Isyaku Yau, Rabiu Sani, da Nata’ala Sani.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana farautar uku da suka gudu.

Advertisement

Ana zargin sun kashe Shehu Abubakar, mai shekaru 25, a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin Sarkin ‘Ya, a karamar hukumar Bagwai da ke yankin arewacin jihar Kano.

Premium Times ta ruwaito cewa Manoman sun tare hanya sun hana shanun da makiyayin wucewa, daga nan ne rikici ya kaure a tsakanin su. Manoman suka kashe makiyayin da shanun sa 97 sanan wasu shanu 91 suka arce har yanzu ba a san inda suke ba.

Advertisement

Mai gabatar da kara ya bayyana cewa an kiyasta adadin shanun da aka kashe da kuma wadanda suka bata ya kai Naira miliyan 102.7.

Wadanda ake tuhumar dai sun musanta aikata laifin.

Advertisement

A Wani Labarin kuma An Samu Rahoton Tashin Gobara A Jahar Kaduna Sau 33 Cikin Watan Nuwamba 

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending