Connect with us

News

Majalisar Dokokin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Kudi Kimanin Naira Bilyan 6 Domin Gina Rukunin Gidaje 1,500  

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi kimanin Naira Bilyan 6 domin gina rukunin gidaje 1,500 da nufin rage karancin gidaje a Jihar Jigawa.

Advertisement

Kwamishinan yada labarai, Matasa,Wasanni da al’adu na jihar Jigawa Sagir Musa shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar dattawa ta tantance alkalai 11 na kotun koli

Sagir Musa yace gidajen da za’a gina sun kunshi gidaje masu dakuna uku-uku a ciki, da gidaje masu dakuna biyu-biyu sare a wasu sassana Jihar nan.

Advertisement

 

Yace wannan aiki yayi dai-dai da manufofin 12 na gwamnatin Gwamana Malam Umar Namadi domin ‘Yan jihar jigawa su samu saukin rayuwa.

Advertisement

Kwamishinan yace tuni aka fitar da kudi kimanin Naira Bilyan 5.9 domin fara aikin.

 

Ya kara da cewa za’a gina rukunin gidaje 600 a babban Birnin Jiha Dutse,da rukunin gidaje 200 a Hadejia da 100 a Kazaure sai kuma kananan hukumomin Gumel, Ringim da Birnin-Kudu. Yace za’a gina gidajen guda 150-150 a kananan hukumomin Babura da Kafin-Hausa da nufin magance karancin muhalli a jihar Jigawa.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending