Connect with us

News

Masu jiran a zartas masu da hukuncin kisa sun kai mutum 3,413 -Jami’in Kurkuku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Najeriya, ta bayyana cewa waɗanda ke tsare kuma suke jiran a zartas masu da hukuncin kisa, sun kai mutum 3,413.

Haka dai Kakakin Yaɗa Labarai na Hukumar Gidajen Kurkuku na Najeriya, Abubakar ya bayyana.

Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su kamar Bayi a Sokoto

Umar ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma’a, a Abuja.

Ya ce daga cikin ɗaurarru 77,849 da ke tsare, 76,081 duk maza ne, 1,768 su ne mata.

Ya ce wannan lissafi na zuwa har ranar da 18 ga Disamba, 2023 ne.

Advertisement

Umar ya ce fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Najeriya.

Premium Times ta ruwaito cewa akwai sama da mutum 50,000 tsare a kurkuku daban-daban cikin ƙasar nan, waɗanda ke zaman tsammanin jiran a yanke masu hukunci a kotuna daban-daban.

Wani jami’i ne ya tabbatar da haka, inda ya ce kashi 69 bisa 100 na waɗanda ke tsare a gidajen kurkuku, duk jiran a yanke masu hukunci suke yi.

Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Najeriya (NCoS), ta ce akwai mutum 53,836 tsare a gidajen kurkuku daban-daban, waɗanda ke zaman jiran a yanke masu hukunci a gidajen kurkuku 253 da ke cikin ƙasar nan.

Wannan ƙididdiga dai za ta iya ƙaruwa, domin an yi lissafin adadin su ne iyar ranar 18 ga Disamba.

Kakakin Yaɗa Labarai na Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Ƙasa, Abubakar Umar ne ya bayyana haka, yayin ganawar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Alhamis, a Abuja.

Advertisement

Umar ce taƙaitaccen lissafin adadin masu jiran yanke hukuncin da waɗanda aka yanke wa, su 77,849 ne a faɗin ƙasar nan.

Ya ce waɗanda aka yanke wa hukunci su 24,013 ne, tare da yin ƙari da cewa maza waɗanda aka yanke wa hukuncin zama gidan kurkuku su 23,569 ne, mata kuwa 444.

Ya ce ƙididdiga ta nuna kashi 69 bisa 100 na waɗanda ke tsare gidajen kurkuku, duk yanke hukunci su ke jira, sauran kashi 31 ne aka yanke wa hukunci,” inji shi.

Umar ya ce babban abin da ya fi damun gidajen kurkuku a ƙasar nan ita ce yawan cinkoson ɗaurarru a gidan kurkuku, wanda cikin matsalolin da ke haddasa hakan, har da rashin ɗakunan aniyar masu laifi wadatattu kuma na zamani.

Ya ce yawancin ɗakunan duk tsoffin gini ne, kuma sun yi kaɗan.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta ƙara gina ɗakuna 3,000 a gidajen kurkuku daban-daban, ciki har da Kano, yayin da ɗakunan kurkukun Abuja da Fatakwal ana kan aikin su, an ma kusa kammalawa.

Advertisement

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira miliyan 585 domin biyan tarar da kotuna suka yanka wa wasu ɗaurarru. Ya ce ta haka za mu samu sauƙin cinkoso sosai, idan aka saki waɗanda ke zaman kasa biyan tarar da kotu ta aza masu.

Ya kuma jinjina wa ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi domin sakin ɗaurarru 4,068.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending