Connect with us

News

Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke Jihar Filato

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke Jihar Filato a yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Kamfanin dilancin labarai na AFP wanda ya ce rundunar sojin ƙasar ce ta tabbatar masa da harin, ya rawaito Kyaftin Oya James ya shaida mata cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Asabar.

Advertisement

Yan Nijeriya Na Shan Bakar Wahala Saboda Rashin Iya Mulki -Obi

Rikicin kabilanci da kuma na manoma da makiyaya ya zama tamkar ruwan dare a Jihar Filato, wanda aka shafe shekaru ana fama da shi, kuma yana yawan jawo asarar rayuka.

“Muna barci sai kwatsam muka ji wata ƙara mai ƙarfi,” in ji wani mazaunin ƙauyen Markus Amorudu.

Advertisement

“Mun tsorata sosai saboda ba mu tsammaci wani hari ba. Mutane sun ɓuya, amma maharan sun kama da yawa daga cikinmu, an kashe wasu an jikkata wasu,” a cewar ganau din.

Har yanzu ba a gano musabbin kai harin ba, sannan ba a san waɗanda suka kai shi ba.

Advertisement

Sai dai tuni aka aika jami’an tsaro don kare ɓarkear rikici a yankin, inda ake yawan samun hatsaniya tsakanin makiyaya da yawancinsu Musulmai ne da kuma manoma da yawancinsu Kiristoci ne.

Gwaman Jihar Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da wannan hari yana mai kiransa “mummunan da bai kamata ba,” tare da shan alwashin gano waɗanda suka kai shi da kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

Advertisement

“Gwamnati za kuma ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile hare-haren da ake kai wa kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba,” kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Gyang Bere ya gaya wa manema labarai.

A wani labarin kuma Yan Nijeriya Na Shan Bakar Wahala Saboda Rashin Iya Mulki -Obi

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending