News
Hukumar Lafiya ta duniya WHO na zargin kamfanin India da zamba cikin aminci kan maganin tarin yara
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Hukumar Lafiya ta duniya WHO da gwamnatin Gambia, sun zargi kamfanin harhada magungunan kasar India na ‘Maiden Pharmaceuticals’ da sauya samfuran magungunan tarin da aka mika wa masu bincike don tantance ko su ne sanadin mutuwar yara 70 a kasar Gambia.
A cikin watan Oktoban shekarar 2022 ne gwamman yaran na Gambia suka rasa rayukansu, bayan shan maganin tarin kamfanin na India, wanda bayan gudanar da bincike hukumar WHO ta ce magungunan sun kunshi gubar da ta yi sanadin salwantar rayukan da dama.
Hukumar Yan Sanda Ta Karyata Batun Karbar Naira 2,000 Daga Hannun Masu Neman Aikin
A baya bayan nan ne dai wasu majiyoyi suka bankado zargin cewa, akwai wasu jami’an binciken na India da suka karbi cin hancin Rupee miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka dubu 600,000, inda suka sauya samfuran magungunan da za a bincika kafin mika su ga babban dakin binciken kasar, lamarin da ya sa sakamakon da aka fitar ya ci karo na da hukumar WHO.
Fri ta ruwaito cewa Tun a karshen makon jiya ne dai, kamfanin na ‘Maiden Pharmaceuticals’ ya musanta zargin da ake masa na bayar da cin hanci don sauya bayanan magungunan tarin da suka yi sanadin mutuwar gwamman yara.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
