News
Gobara Ta Kone Shaguna 22 Tare Kadarori Na Miliyoyin Kudi A Kasuwar Gwarzo Dake Jihar Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An lalata kadarori na miliyoyin naira a wata gobara da ta tashi a kasuwar Gwarzo dake jihar Kano
‘Yan kasuwar da abin ya Shafa sunyi Kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su kawo musu dauki domin rage musu radadin da suke ciki
Kafin Kashe Gobarar data tashi sai da aka Dauki lokaci Mai Tsawo ana fafatawa
Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Masu Nauyin Kilogram 100,458 A Jihar Kaduna
An lalata kadarori na miliyoyin naira a wata gobara da ta tashi a kasuwar Gwarzo dake karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.
Gobarar da ta afku a ranar Litinin, ta jefa wadanda lamarin ya rutsa da su cikin mawuyacin hali inda aka ce da yawa daga cikinsu sun yi asarar miliyoyin nairori a sanadiyyar bala’in.
Jami’in yada labarai na shiyyar na karamar hukumar Gwarzo, Rabiu Khalil ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
“Gobarar ta tashi ne da tsakar daren Lahadin da ta gabata kuma ta dauki jami’an hukumar kashe gobara ta jihar har zuwa safiyar Litinin kafin su iya kashe ta,” in ji sanarwar.
Khalil ya bayyana cewa gobarar ta kone shaguna da dama gaba daya, yayin da aka lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.
Sai dai ya bayyana cewa babu wani rauni ko asarar rai a lamarin.
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Dayyabu Bala, ya ce ya yi asarar dukiya ta sama da Naira miliyan 5 sakamakon gobarar.
Ya yi kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su kawo musu dauki domin rage musu radadin da suke ciki.
Wani mamba mai wakiltar mazabar Gwarzo ta tarayya, Abdulahi Babangandu, ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa inda ya bayar da tallafin Naira 500,000 ga wadanda abin ya shafa.
Majiyar Jaridar INDA RANKA da ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta lalata shaguna 22.
Abdullahi, ya bayyana cewa daga cikin shaguna 22, biyu ana kan gina su a kasuwar.
“Yawancin shagunan da abin ya shafa 22 ne daga cikinsu biyu ba a kammala Su ba,” in ji Abdullahi
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
