Connect with us

News

Kisan Filato: Wasu Mata Masu Zanga-Zanga Sun Kone Gidan Wani Basaraken Gargajiya

Published

on

DAGA  HAUWA IBRAHIM 

Wasu fusatattun mata da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kashe-kashen da aka yi a wasu kauyuka a jihar Filato a ranar Juma’a, sun kona gidan Hakimin garin Bokkos, Michal Monday Adanchi.

Advertisement

Garin Bakkos da ke karamar hukumar Bokkos na daya daga cikin al’ummar da aka yi wannan kashe-kashen.

Gwamnatin Taraya Ta Saki Kudi Naira Bilyan 50 Domin Kammala Wasu Ayyuka A Abuja

An tattaro cewa an kona gidan hakimin da misalin karfe 12:30 na ranar Juma’a.

Advertisement

An ce matan sun fusata ne sakamakon kame wasu daga cikin al’ummar da ake zarginsu da hannu a kisan.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa, “al’amarin ya faro ne a ofishin ‘yan sanda, inda su [matan] suka nuna bacin ransu game da kama wasu daga cikin al’ummar yankin.

Advertisement

“Bayan sun bar ofishin ‘yan sandan ne suka zarce zuwa gidan basaraken, inda suka nuna rashin amincewarsa da cewa shi dan kasuwa ne, bayan ‘yan mintoci kadan da isa gidan sai suka banka masa wuta,” inji ganau ya kara da cewa.

Sai dai yadda zanga-zangar ta yi kamari ta kai ga isowar sojoji wadanda suka tarwatsa matan masu zanga-zangar.

Advertisement

The Nation ta ruwaito cewa  rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cafke mutane takwas da ake zargi da kai hare-haren.

A hare-haren da aka kai kimanin kauyuka 23 tsakanin ranakun 24, 25 da 26 ga watan Disambar 2023, Rahotanni na nuni da cewa, an kashe mutane sama da 200, da jikkata wasu da dama, tare da kone daruruwan gidaje.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending