News
Yan Ta’adda Sun Yi Wa Matar Aure Yankan Rago A Jihar Yobe
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Ana fargabar cewa ’yan ta’adda sun kashe wata matar aure mai suna Ammi Adamu Mamman a gidan mijinta da ke rukunin gidajen Bra-Bra na Karamar Hukumar Damaturun Jihar Yobe.
Bayanai sun ce maharan sun kashe matar mai shekaru 42 ta hanyar yankar rago.
Shugaba Tinubu ya buƙaci hafsoshin tsaron Najeriya su kakkaɓe matsalar rashin tsaro a ƙasar
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Aminiya ta ruwaito cewa DSP Dungus ya ce hukumar binciken manyan laifuka ta jihar ta fara gudanar da bincike domin zakulo masu hannu a wannan aika-aika.
Advertisements
