Connect with us

News

Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano Ta Kafa Kwamitin Da’a Da Ladabtarwa Kan Lafiya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A kokarinta na cika wani bangare na ayyukanta na tabbatar da isasshiyar kariya ga lafiyar al’ummar jihar, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta kaddamar da wani babban kwamitin da’a da ladabtarwa kan harkar kiwon lafiya.

Advertisement

Da yake kaddamar da kwamitin, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce gwamnatin jihar Kano na karbar bayanai masu dimbin yawa da ke nuna yatsa ga wasu ma’aikatan lafiya da aikata wasu ayyukan rashin da’a da ke jefa marasa lafiya cikin kunci.

Mun damu akan yadda Najeriya ke ta durkushewa a tsarin dimokuradiyya da kuma matsalar tsaro -Northern States Civil Society Networks 

Dakta Labaran ya tabbatar da cewa ma’aikatar ba za ta nade hannunta ba, ta bar rayuwar jama’a cikin barazana ba, inda ya koka da cewa hakan ya saba wa kudiri da kokarin Alhaji Abba Kabir Yusuf na tabbatar da ingantacciyar lafiya da walwala ga al’ummarsa ba

Advertisement

“Don shawo kan wannan matsalar, na ga ya zama wajibi a kan kaina na kafa kwamiti na dindindin wanda zai rinka bincikar duk wata matsala ta lafiya da ta addabi jama’armu da nufin magance ta gaba daya.

“Ina so in sanar da jama’ar jihar Kano cewa rayuwarsu na da matukar muhimmanci a wurin Mai Girma Gwamna, kuma a matsayinmu na masu kula da harkokin kiwon lafiya, hakkinmu ne mu kiyaye ta.” Ya jaddada.

Advertisement

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Ibrahim Abdullahi ya sanya wa hannu aka turawa da Jaridar Inda Ranka kwamishinan ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru ba tare da fargaba ba domin kare rayuwar jama’a ta hanyar rashin barin ana keta da’a da ka’idar aikin lafiya da zai kai ga cutar da rayuwar jama’a.

Ya kuma yi kira gare su da su duba batun karkatar da majinyata daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu da ake yawan samu, har ma da duk wasu abubuwan da suke ganin za su taimaka wa gwamna mai kishin lafiya wajen cimma kyawawan manufofinsa kan tsarin kiwon lafiya.

Advertisement

 

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa kwamitin zai rika sauraron korafe-korafen al’umma game da harkar lafiya tare da daukar matakin ladabtarwa da mutane za su yi alfahari da shi, don an zabo mambobinsa ne bisa la’akari da tarihinsu na hidimta wa al’umma.

Advertisement

 

Da yake mayar da jawabi, Shugaban Kwamitin wanda kuma shi ne Darakta Janar na Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA), Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya tabbatar wa Dakta Labaran cewa za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun dakile lalaci da sauran ayyukan rashin da’a da ke kawo cikas ga lafiyar mutane a duka asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

Advertisement

 

Ya kuma yaba wa Kwamishinan bisa amincewar da ya yi musu ya ba su wannan nauyi, inda ya kuma ba shi tabbacin za su yi aikin ba tare da nuna bambanci ba, kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa dokoki da ka’idojin kiwon lafiya.

Advertisement

 

Mambobin kwamitin sun hada da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Manyan Asibitoci Dr. Mansur Mudi Nagoda da Ko’odinetan Cibiyar Yaki da Cututtuka ta jihar Kano Farfesa Muhammad A. Abbas da kuma Shugaban Kwamitin Da’a da Ladabtarwa na Kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano Farfesa Usman Idris Takai.

Advertisement

 

Sauran sun hada da Daraktan Kula da Ayyukan Likitoci na Ma’aikatar Dr. Shehu Abdullahi Usman, Pharm. Aliyu Adamu ma’aikacin gwamnati mai ritaya, Dakta Tanko Zakari daga Kungiyar Daraktocin Lafiya, Wakili daga Hadaddiya Kungiyar Sashin Lafiya ta Najeriya (JUHESU), yayin da Daraktan Kula da Ma’aikatan Jinya na ma’aikatar Abdullahi Garba Harbau zai kasance Sakatare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending