Sports
AFCON 2023: Nijeriya Ta Buga 1-1 Da Kasar Equatorial Guinea
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga canjaras a wasanta na farko a gasar AFCON ta bana inda ta buga da kasar Equatorial Guinea a filin wasa na Olympic Alassane Outara da ke birnin Abidjan.
Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salbado ne ya fara jefa kwallo a ragar Nijeriya a minti na 36 da fara wasan.
Cutar Bakon Dauro Ta Yi Ajalin Yara 190 A Najeriya Daga 2022 Zuwa Yanzu – Hukumar NCDC
Yadda Aikin Gine-gine Na Kasar Sin Suka Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka
Amma minti biyu tsakani Victor Osimhen ya farke wa Nijeriya kwallonta inda ya jefa kwallon da Ademola Lookman ya bashi a ragar abokan karawar.
Hakan yasa Nijeriya ta koma matsayi na uku a rukunin A na gasar AFCON.
Advertisements
