News
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 2 Na Jami’ar Al-Qalam
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
‘Yan bindiga sun sace wasu dalibai mata biyu na Jami’ar Al-Qalam da ke Jihar Katsina.
Wadanda lamarin ya rutsa da su, su ne Habiba Ango Shantali da Maryam Abubakar Musa.
Mustapha ya taya Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli
Lamarin ya faru ne yayin da daliban ke kan hanyar komawa makarantar a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024.
Shugaban Kungiyar Daliban Jihar Neja (NANISS) na kasa, Kwamared Gambo Idris Shehu, ya tabbatar da sace daliban a wata sanarwa da sakatare-janar na kungiyar, Kwamared Mohammed Ibrahim ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun samu labarin sace wasu dalibanmu biyu na Jihar Neja da ke karatu a Jami’ar Al-Qalam a Jibar Katsina a kan hanyarsu ta komawa makaranta.
“Daliban da aka sace su ne Habiba Ango Shantali da Maryam Abubakar Musa,” in ji sanarwar.
“Muna rokon Allah Ya kubutar da su daga hannun wadanda suka sace su.”
