News
Kotu ta yanke hukuncin mayar wa Najeriya fam miliyan 6.9 da aka sace
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukuncin kotun ya ce za a iya maido wa Najeriya kadarorin satar da darajarsu ta kai £6.9m ($8.9m).
Hakan ya zo ne bayan atoni-janar na Jersey ya miƙa wa kotun Ingilar da ke tsibirin takardar sallamawa a watan Nuwamba.
Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukunci akan zaɓen Nasarawa
Kotun ta yanke hukuncin cewa kuɗaɗen da aka ajiye a wani asusun banki a Jersey, akwai yiwuwar jami’an gwamnatin (Goodluck Jonathan) da ta yi mulki a shekarar 2014 ne suka sace su.
Bbc ta ruwaito cewar Za a yi yarjejeniya da gwamnatin Najeriyar kan maido da kuɗaɗen.
An tura kuɗaɗen ne inda aka fake da cewa na wasu kwangilolin sayen makamai ne da gwamnati ta amince da su a lokacin rikicin Boko Haram a ƙasar, tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015.
‘MUTANEN DA AKA ZALUNTA’
Gwamnatin Jersey ta ce akwai yiwuwar mafi yawan kuɗaɗen an yi niyyar sayen makamai da su ne, amma aka karkatar da aƙalarsu ta asusun bankunan ƙasar waje ta hanyar kamfanonin Shell.
Ofishin babban mai shari’ar ya kuma ce ya yi amanna cewa an ba iyalan jam’iyya mai mulki (PDP) a Najeriya kuɗaɗen, kuma aka rarraba su ga ƴan jam’iyyar a lokacin babban zaɓen 2015.
Haka kuma an yi niyyar amfani da kuɗaɗen ne ta hanyar da “bata dace ba”.
Babban mai shari’ar, Mark Temple KC, ya ce gwamnatin Jersey ta yi aiki “kafaɗa-da-kafaɗa” da gwamnatin Najeriya don ganin an karɓo kuɗaɗen a madadin ƴan ƙasar ta Najeriya.
Ya ƙara da cewa: “Wannan shari’ar tana ƙara nuna tasirin dokar sallamawa ta shekarar 2018 wajen karɓo kuɗaɗen rashawa tare da mayar da su ga mutanen da aka zalunta.
“A halin yanzu na yi niyyar shiga yarjejeniyar yadda za a mayar da kuɗaɗen Najeriya .”
