Connect with us

News

Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano Da OHAI Sun Kulla Yarjejeniya Kan Tiyatar Lebe 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Advertisement

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da Shirin Kula da Lafiyar Baki (Oral Health Advocacy Initiative, OHAI) sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan aikin tiyatar lebe a jihar.

Da yake jawabi yayin sanya hannu a ma’aikatar, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yaba da kasancewar kungiyar a jihar domin sun yi kokari wajen inganta rayuwar wasu mutanen Kano.

Advertisement

Babu Inda Na Ce Na Fi ‘Yan Nijeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa -Aliko Ɗangote

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar, lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan ya bai wa kungiyar OHAI tabbacin goyon baya gwamnatin Kano na su ci gaba da gudanar da ayyukan da suke yi, ya kara da cewa an duba ayyukan da suka yi a baya a jihar kuma gwamnati ta gamsu da hakan, ya kuma bukace su da su ci gaba saboda ana bukatar ayyukan nasu.

Advertisement

Ya yi nuni da cewa, irin wadannan ayyuka na jin kai suna da yawa da gwamnati ita kadai ba za ta iya tafiyar da su ba, yana mai jaddada cewa kasancewar kungiyoyi irin nasu da ke mai da hankali kan wata matsala guda daya tare da magance ta ba shakka zai taimaka matuka wajen taimaka wa mutane da inganta sashin lafiya na jihar.

Ya yi fatan rattaba hannu kan yarjejeniyar zai kara inganta alakar da ke tsakanin gwamnatin Kano da kungiyar ta OHAI ta yadda al’ummar jihar za su kara samun tagomashi a yunkurin gwamnati na kawo sauyi ga fannin kiwon lafiya baki daya don ya dace da tsarin da duniya ke kai.

Advertisement

Tun da farko, babban jami’in kula da shirin OHAI na jihar, Kpam Peter, ya bayyana cewa kungiyar kungiya ce mai zaman kanta da ke da manufar kawar da cututtukan baki da na fuska a Najeriya da Afrika baki daya.

Ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin kungiyar fara da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta fara ne tun a shekarar 2016 inda aka kulla kyakkyawar alakar aiki da ma’aikatar da hukumominta da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Advertisement

Mista Peter ya bayyana cewa, daga shekarar 2016 zuwa 2022, OHAI ta yi wa majinyata 869 tiyatar lebba a fadin kananan hukumomin 44, inda Bebeji ta samu mafi yawan mutane 49, yayin da ba a samu mutum ko daya ba a kananan hukumomin Birni da Gwale, inda ya jaddada cewa an ribanya kokari wajen zaburar da kananan da aka samun karancin fitowar mutane, yana mai gode wa ma’aikatar saboda kyakkyawar tarbar da ta yi musu.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar a gaban Babban Sakatare Alhaji Musa Tanko da Daraktan Kula da Ayyukan Likitoci Dakta Shehu Abdullahi Usman da kuma Mataimakin Daraktan Kula da Ayyukan Likitoci Shehu Umar na Ma’aikatar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending