Connect with us

News

DA ƊUMI-ƊUMI: Kungiyar kwadago ta sanar da yin zanga-zangar a fadin Nijeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Kungiyar kwadago ta ƙasa, NLC ta ayyana yin zanga-zanga ta kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Joe Ajaero, shugaban NLC ne ya bayyana haka a yayin wani taron gaggawa, wanda aka gudanar a yau Juma’a.

Hukumar FCCPC ta rufe ɗaya daga cikin manyan kantunan sayar da kayan masarufi na Sahad Stores

Ajaero ya ce an dauki matakin gudanar da zanga-zangar ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka baiwa gwamnatin tarayya kan ta magance wahalhalun da kasar ke fuskanta.

NLC ta bada wa’adin ne domin a matsa wa gwamnatin Najeriya don ta magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending