News
Sanusi ya ɓarke da kuka a lokacin da yake jawabin ta’aziyyar rasuwar Herbert Wigwe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fashe da kuka a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron karrama marigayi Herbert
Wigwe, tsohon shugaban rukunin kamfanin Access Holdings Plc.
Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka halarci tron bikin karrama marigayin mai shekaru 57, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Sarki Sanusi ya ce ya yi zaton zai riga Herbert mutuwa.
” A nawa lissafin na yi zaton zan riga Herbert mutuwa, amma sai gashi ya tafi ya barmu a duniya.
Bayan haka da sarki Sanusi ya bayyana yadda marigayi Herbert ya tsaya masa tsayin daka a lokacin da gwamnatin Kano ta rantse sai ta ga bayan sa a sarautar Kano.
” A lokacin da na tabbatar ba makawa sai za a cire ni daga sarautar Kano, na kira shi na ce masa, Herbert, sai dai fa ayi hakuri amma babu makawa za a tsige ni daga sarautar Kano.
” A lokacin da aka sanar da tsige ni, da karfe tara na safe kafin 12 na rana, ya aiko da jirgin sama, na saka iyalaina zuwa Legas.
” Da suka sauka Legas, ya ajiye a Otelsaga baya kuma ya saka su a gida. Ya ce min duk abinda nake so yana nan tare da kai.
Bayan haka Sarki Sanusi ya bayyana yadda Herbert ya taimaka masa kan harkokin kuɗaɗensa na ajiya da na asusun ƴaƴan sa na karatu da sauransu.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
