News
Mata Za Su Iya Magance Matsalar Najeriya Idan Aka Basu Tarbiya Mai Kyau Da Kuma Ilimi —Malam Ibrahim Khalil
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Fitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce mata za su iya magance matsalar najeriya idan aka basu tarbiya mai kyau da kuma samun mazaje na gari.
Sheikh Ibrahim Khalil ya baiyana hakan a yayin taro akan Muhimmancin ilimin yayi mata da mai baiwa gwamnan shawara kan ilimin yayi mata Hajiya Hafsat Adahama ta sharya.
Kara da cewa rayuwa ba ta taba ci gaba ba in babu ilimi. Kowace al’umma na kokarin ta ga ta ci gaba wajen samar da ingantaccen ilimi.
Karatun ’ya’ya mata na da matukar amfani, koda a ce sun yi aure hakan ba zai kawo musu wata matsala ba, don sun ci gaba, sai dai ya kara karfafa musu gwiwa wajen samar da ingantacciyar al’umma.
Da ta ke yi wa Jaridar Inda Ranka karin haske babbar maitaimaka wa gwamnan jahar Kano, kan ilimin Yaya Mata Hon. Hafsat Aminu Adhama, ta bayyana cewa sun shirya taron ne domin tara Dalibai Mata da Iyayensu don a wayar mu su da Kai, don su San muhimmancin iliminsu tare da kara zaburar da su wajen dage wa kan karatunsu.
Hafsat Adhama ta Kara da cewa, za su kaddamar wani shiri na Mayar da marayu Mata 500 Makaranta domin dakile su daga yawon tallace-tallace .
” Mun yi taro domin rabo wadannan yaran daga tituna , nan bada Jima wa ba” Hafsat Adhama “.
Adhma ta ce bayan sun kammala wannan aiki za su shiga kauyuka, don gabatar da taro na musamman da shugabanni da iyaye, Sarakuna da kuma Mallamai don su fahimci kudirinsu na kai Ya mace Makaranta maimakon ta kare a yawon Talla.
A cewar ta shirin nan na AGILE da ake bayar da tallafin Kudi duk Wata ga Dalibai matan, zai Samar da daidaito wajen Hana su zuwa talla, domin wa su idan an Hana su zuwa talla suna kafa hujjar cewar tallan shi ne yake rike su , amma za su yi kokarin wayar da su kan muhimmancin yin ilimi.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
