Connect with us

News

Zaftarewar kasa yayi Sanadiyyar Mutuwar  almajirai guda 8 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Akalla yara almajirai guda 8 zabtarewar kasa ta kashe a Birnin Kebbi a  lokacin da suka je aikin saran kasar da za’ayi amfani da ita domin aikin gini.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa lamarin iftila’in yafaru yau asabar da safe lokacin da almajiran suke je gudanar da wannan aiki domin yin gini.

Kantoman karamar hukumar Birnin Kebbi Mohammed Dahiru Ambursa ya tabbatarwa da Radiyo Faransa  aukuwar lamarin da kuma mutuwar wadannan almajirai guda 8 wadanda suka fito daga sassan jihar domin koyon karatun Alkur’ani a birnin.

Advertisement

Ambursa ya ce da misalin karfe 2 na ranar yau ake saran yiwa wadannan yara jana’iza, yayin da wasu guda 3 kuma ke can asibiti ana kula da lafiyar su saboda raunin da suka samu.

Kantoma yace tuni suka bada umarnin killace wurin da aka samu hadarin da kuma shelar hana aiki a wurin.

Advertisement

Ambursa ya kuma jajantawa iyayen wadannan yara da suka rasa rayukansu, tare da bai wa uwayen kasa umarnin shelar hana ginan kasa a wannan wuri.

Sanya yara almajirai aikin karfi domin samun abinda za su ci ba sabon abu bane a sassan arewacin Najeriya, abinda ya sa kungiyoyi da dama ke kiran sake fasalin koyon karatun Alkur’ani ta yadda iyaye zasu dinga daukar nauyin ciyar da ‘yayan su, yayin da suke daukar karatun a gaban malamai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending