News
Barawon Da Ya Caka Wa Wata Budurwa Wuka Ya Kwace Wayarta Ya Fada Komar ’Yan Sanda
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Barawon da ya caka wa wata budurwa wuka ya kwace wayarta a garin Damaturu na Jihar Yobe ya fada komar ’yan sanda.
A kwanakin baya ne dai wani barawon waya ya kwace wayar budurwar bayan da ya caka mata wuka a gidan baya a unguwar Malari a garin Damaturu fadar.
Sojojin Rasha Sun Shiga Sansanin Dakarun Amurka A jamhuriyar Nijar
Sakamakon haka aka garzaya da ita babban Asibitin koyarwa na jihar inda a halin yanzu take samun kulawa.
Aminiya ta ruwaito cewa a wata sanarwa, kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, ASP AbdulKareem Dungus ya ce jami’an su sun kama matashin.
A cewarsa, wayar da barawon ya kwace samfurin Itel ce hade da da layi a ciki.
Dungus ya ce za a ci gaba da bincike daga bisani a tura matashin zuwa kotu don fuskantar hukuncin da ya ya daidai da laifinsa, domin hakan zama izina ga na baya.
