News
Yau ce ranar ‘yan jarida ta duniya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yau ce ranar ‘yan jarida ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin tunawa da irin gudunmuwa da kuma rawar da ‘yan jarida ke takaw a wajen bayar da labaran abubuwan da ke faruwa a duniya.
An dai kebe kowacce ranar 3 ga watan Mayu na kowacce shekara domin jinjinawa ‘yan jarida a duniya.
Barawon Da Ya Caka Wa Wata Budurwa Wuka Ya Kwace Wayarta Ya Fada Komar ’Yan Sanda
Taken ranar na bana dai shi ne ” Aikin jarida ba tare da tsoro ko Alfarma ba”.
‘Yan jarida a fadin duniya na fuskantar kalubale iri-iri a wannan lokaci da kasashen duniya
Yasir Sani Abdullahi, dan jarida ne kuma shi ne shugaban kamfanin jaridar Inda Ranka a Najeriya , cewa, ayan jarida na da babbar rawar takawa wajen tabbatar da suna samar da sahihan labarai ga al’umma.
Ya ce ko shakka babu aikin jarida ya kara muhimmanci a wannan lokaci bisa la’akari da yadda kafafan sada zumunta ke taka rawa wajen yada labaran bogi.
Yasir Sani, ya ce ” Dole ne ‘yan jarida suka rinka yin taka tsan-tsan a wannan lokaci, saboda yadda jama’a musamman ma’abota shafukan sada zumunta ke yada labarai marassa tushe”.
Ya ce to yanzu a wannan yanayi, ‘yan jarida dama kafafan yada labarai sun mayar da hankali ne wajen tantance ainihin labaran gaskiya fiye da da.
