News
Gwannatin Tarayya Ta Koka Akan Halin Da ‘Yan Jarida Ke Ciki Wajen Gudanar Da Aiyukansu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta ce ‘yan jarida a kasar nan na gudanar da aiyukan su cikin mawuyacin yanayi, wanda suka cancanci a inganta masu yanayin gudanar da aiyukansu.
Ministan yada labarai da wayar da kai na kasa, Alhaji Mohammed Idris ne ya baiyana haka yayin hirarsa da kanfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abuja.
Ya ce yan jarida da dama na sadaukar da rayuwarsu wajen gabatar da aiyukansu, inda y ace zai yi amfani da damarsa wajen ganin an inganta walwalar yan jarida a kasar nan.
Ya kuma kara da cewar ‘Yan jarida mallakin kasar nan ne, wanda Najeriya ya kamata ta yi wani abu na ciyar da likafarsu gaba, ta bangaren biyan albashi da sauran wasu abubuwa.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Ƙauyen Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
