Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Ƙauyen Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kwashe wani adadi da jama’ar kauyen Yola da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan daban daji sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na kauyen.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Zata Yi Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 26 A Shekara Mai Zuwa Ta 2024

Bayanai sun ce hare-haren da aka kai yankuna daban-daban sun yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama yayin da aka yi garkuwa da wasu.

 

Advertisement

A cewar wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, hare-haren sun auku a yankuna daban-daban na kauyen da ba zai iya fayyace adadin mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba.

 

Advertisement

“Na samu labarin cewa a rana ta farko sun sace mutum huud sannan sun kashe wasu mutum biyu.

 

Advertisement

“Haka kuma a rana ta biyu sun kashe karin wasu mutum biyu tare da garkuwa da mutum daya.

 

Advertisement

“Sai dai ba ni da tabbaci kan alkaluman mutanen da aka sace ko aka kashe.

 

Advertisement

“Amma ba na tantamar cewa an dauke wasu mutane kuma an kashe wasu.

 

Advertisement

 

“Abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne Karaye tana bukatar dakarun soji su kawo mana dauki saboda wadannan hare-hare,” a cewarsa.

Advertisement

 

Rahotanni sun bayyana cewa, a bayan nan yankunan Karamar Hukumar Karaye da Rogo na fuskantar matsalolin tsaro saboda kusancinsu da Jihohin Kaduna da Katsina.

Advertisement

 

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne wasu ’yan daban daji suka kashe wani mutum daya tare yin garkuwa da wani dan kasuwa a Kauyen Gangarbi da ke Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Nasiru Na’ayya.

Advertisement

 

Kazalika, a shekarar 2021 ce Masarautar Karaye ta yi koken yadda ake samun kwararowar masu hakar ma’adanai daga Jihar Zamfara.

Advertisement

 

Wasu majiyoyi sun ce tuni masarautar ta dauki matakam da suka dace domin yi wa tufkar hanci.

Advertisement

 

Sai dai ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayarsa ba har z

Advertisement

uwa lokacin hada wannan rahoto

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending