News
Shugaban Tunisia na kama ‘yan jarida da masu hamayya da gwamnatinsa
‘Yan sanda a Tunisia sun kama shugaban wani gidan rediyo a rana ta uku na kamen ‘yan siyasa da masu fafutika.
Wakiliyar BBC ta ce, Mahukunta sun kai sumame gidan Noureddine Boutar, na tashar Mosaique FM, da ke yawaita watsa shirye-shirye da ke caccakar shugaban kasar Kais Saied.
Tun ranar Asabar, ‘yan sanda suka kama wani hamshakin ɗan kasuwa, Kamal Eltaief, da fitaccen ɗan siyasa, Khayam Turki, da wani jigo a jam’iyyar hamayya, da wasu alkalai biyu da tsohon jami’in diflomasiyya.
Yayin da ake nuna damuwa kan ‘yancin siyasa, Shugaba Kais Saied ya kare matakinsa, da ya ce ya yi daidai da doka, kuma hakan yana da amfani domin kare Tunisia daga faɗawa cikin rikici.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
