News
Mai Martaba Sarkin Kano Ya Buƙaci A Dawo Da Makarantar Sojojin Sama Ta Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayaro, ya yi kira ga Shugaban sojojin sama na Nijeriya kan ya yi ƙoƙari wajen dawo da Makarantar Sojojin sama da ke garin Kwa a yanki Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa wadda aka rufe sakamakon rashin tsaro a watannin baya.
Basaraken ya yi wannan kira ne lolacin da Shugaban Sojojin Sama na Nijeriya, Hassan Bala Abubakar, ya ziyarce shi a fadarsa a ranar Alhamis.
Ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya tura wa Blueprint Manhaja ya ce, Sarkin ya ƙara da cewa, makarantar tana da muhimmanci ga al’ummar Jihar Kano da Arewacin Nijeriya baki ɗaya.
Daga nan, Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya Shugaban Sojojin Sama (Chief of Air Staff) murnar samun wannan matsayi na shugabancin sojojin sama na Nijeriya, inda ya yi fatan matsayin nasa zai taimaki al’ummar Kano da Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.
Da yake nasa jawabin, Shugaban sojojin sama na Nijeriya, Hassan Bala Abubakar, ya bayyana wa Sarkin cewa, a matsayinsa na ɗan asalin Jihar Kano ya zo ne ya gabatarda kansa da kuma matsayin da ya samu, sannan su nemin haɗin kan Masarautar Kano wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasa baki ɗaya.
Ziyarar Shugaban Sojojin Saman ta samu rakiyar manyan jami’an tsaro da sauransu.
