Connect with us

News

Tarihin Abubuwan Da Suka Auku A Rana Irin Ta Yau 05 Ga Watan Mayu

Published

on

Marigayi Alh. Umaru Musa 'Yar Aduwa

 

‘Yan Najeriya Na Alhinin Cika Shekaru Goma Sha 14 Cif-cif Da Rasuwar Marigayi Alh. Umaru Musa ‘Yar Aduwa Wanda Ya Rasu Ranar 05/05/2010 bayan fama da rashin lafiya.

Advertisement

Alhaji umaru Musa ‘yar aduwa shine shugaban kasar najeriya na uku da ajali ya riske shi yana kan karagar mulki.

Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi –Gwamnatin Tarraya 

Ya rasu kwanaki kadan da dawo dashi daga kasar saudia inda ya shafe watanni yana jinya awani asibiti dake kasa me tsarki ,wanda hakan ya jawo cece-kucen da dole aka dawo dashi batareda kowa ya gan shi ba har zuwa rasuwar sa.

Advertisement

Kadan daga cikin furucin da marigayi ya yi mai sosa zuciya lokacin yana raye

“Duk lokacin dana tuna ina kara sanin cewa duniya ba gurin zama bane kuma rayuwa babu tabbas.

Advertisement

Yace ni mutum ne kamar kowa bani da bambanci da talaka ko mai kudi cuta kuma daga Allah take shi ke kashewa kuma shi ke rayawa.

Zan iya mutuwa kuma zan iya rayuwa, zan iya mutuwa yau, zan iya mutuwa gobe, zan iya mutuwa mako mai zuwa, zan iya mutuwa wata mai zuwa ko shekara mai zuwa, kuma wata kila zan iya rayuwa har tsawon shekaru casa’in Allah ne kade masani.

Advertisement

Hakika yaku “yan uwana musani cewa duniya ba gurin zama bane babu me tabbata acikinta kowa sai ya mutu.”

Allah ka yi masa gafara tare da sauran mamatan mu, Allah kasa idan ajalinmu yazo mucika da imani

Advertisement

 

Haka zakika a rana mai kamar ta yau Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Anambra, C. C. Onoh, ya rasu yana da shekaru 82. Onoh, wanda lauya ne, ya tsaya takarar gwamnan jihar a shekarar 1983 a karkashin rusasshiyar jam’iyyar NPN, ya kuma doke Jamiyyar (NPP)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending