News
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sauke Shugaban Hukumar Tara Haraji Ta Jihar Kano (KIRS) Daga Mukaminsa
DAGA YADIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Dr. Zaid Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS).
Gwamnan ya kuma amince da nadin Kassim Ibrahim a matsayin daraktan zartarwa na hukumar tara kudaden shiga.
Hukumar gudanarwa ta Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Kocin Kungiyar Abdu maikaba
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce sabon tsarin gudanarwar zai fara aiki nan bada dadewa ba yayin da tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Kano Alh. Sani Abdulkadir Dambo ya koma aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
