Connect with us

News

Akalla Mutane Takwas Ne Suka Mutu Yayin Da Wani Gini Ya Rushe A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Akalla mutane takwas ne ake fargabar suka mutu bayan da wani gini mai hawa daya ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Advertisement

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Ranar Juma’a a yayin da ma’aikata ke aikin ginin.

Shirin Arewa Na Tsige Shugaba Tinubu Daga Mulki Zai Iya Wargaza Najeriya – Shehu Sani

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa akalla mutane 15 ne ciki har da mai ginin suka makale a lokacin da tsarin ya faru.

Advertisement

Maigidan, wanda ake kira Sharu, yana gina sabon bene don haɗa gidan da yake da shi.

Rahotanni na nuni da cewa wasu  daga cikin mutanen da suka makale  a cikin gini sun zu  wucewa ne da suka nemi mafaka  saboda ruwan sama.

Advertisement

An bayyana cewa an garzaya da mutane bakwai asibitin kwararru na Murtala Muhammad, kuma mutum daya ya mutu a kan hanyar.

Wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ta Kano da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa ginin ya makale da  mutane 15, inda ya zuwa yanzu mutum bakwai suka mutu.

Advertisement

Masana na dora alhakin rushewar gine gine akan rashin kwarewar masu gini ko zargin amfani da kaya marasa inganci musamman a Wannan lokacin na tsadar rayuwa..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending