Connect with us

News

Tsadar Rayuwa: Ina Guje Mana Fushin Talakawa —Sanata Ahmad Lawan Ya Gargaɗi Gwamnati 

Published

on

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan,

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya gargadi gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar karancin abinci da kuma karin kudin wutar lantarki domin kaucewa zanga-zangar talakawa da ka iya jefa kasar cikin rudani.

Advertisement

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Gargadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da al’amura ke kara tabarbarewa a Kenya, inda zanga-zangar adawa da matakin da gwamnati ta dauka na kara haraji ta rikide zuwa neman ingantaccen shugabanci da kuma rajin cewa shugaba William Ruto ya yi murabus.

Hukumar NERC za ta hukunta kamfanonin rarraba lantarki kan karancin wuta a Najeriya

Sanata Lawan (APC/Yobe ta Arewa) ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar a jiya Talata, yayin da ya ke bayar da gudunmawa ga kudirin da Sanata Karimi Sunday Steve (Kogi ta Yamma) ya mika tare da Sanata Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) kan “bukatar gaggawar a magance matsalar karancin abinci da kuma hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya.”

Advertisement

Ya bayyana matsananciyar yunwar da ƴan Najeriya ke fuskanta tare da jaddada wajabcin majalisar dattawa ta gaggauta shigar da bangaren zartarwa kan lamarin.

Lawan ya ce, “Idan ba mu dauki matakin gaggawa kan karin farashin abinci da kudin wutar lantarki ba, ba za mu ji dadi ba irin abinda za mu gani a kan tituna ba. Ba za ta yiwu mu dau wannan lokacin muna wulakanta al’umma ba. ”

Advertisement

Ya kuma lura cewa rumbunan kasar nan babu komai a ciki kuma shigo da kayan abinci ya zama matsala saboda tashin darajar kuɗaɗen kasar waje.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending