News
Jami’an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara A Dajin Maƙarfi
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Jami’an Hukumar tsaro ta DSS a Kano sun kama ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara. Yayin artabun guda daga cikin masu garkuwar ya mutu wani wanda ake zargi da kuma samun kudi har ₦26.5 miliyan.
Wani babban jami’i a hukumar DSS ya bayyana cewa, tawagar musamman ta DSS, bisa ga bayanan sirri masu inganci, sun kama wata tawaga ta ‘yan bindiga biyar a dajin Maƙarfi yayin da suke raba kuɗin fansa. An kama ɗaya daga cikin su, Hamisu Tukur, da raunin harbin bindiga, yayin da aka kashe wani wanda ake zargi, Bature.
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna su tura kudaden asusun da suka daina aiki
Lamarin sacewar ya faru ne makonni uku da suka gabata lokacin da wasu ‘yan bindiga suka shiga gidan Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar Rarara, a Kahutu, suka yi garkuwa da ita.
Ta samu ‘yancinta bayan ta shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa.
